Zamu Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro A Kasuwar Kantin Kwari.. Abba Bello

Alhaji Abba Bello Tare Da Tsoffin Shugabanin Kasuwar Kwari Bayan Sun Kawo Masa Ziyara

Daga Nasiru Salisu, Kano
Biyo bayan rashin tsaro da ya addabi Kasuwar Kantin Kwari dake jihar Kano a Arewacin Nijeriya, Hukumar Gudanarwa Kasuwar wato ” Kantin Kwari Market Management Board” ( KKMB) ta sha alwashin kawo karshen matsalar rashin tsaro a Kasuwar.
Hukumar tace tuni ta fara Sanya manyan kofofin shige da fice a sassa daban-daban na Kasuwar domin tabbatar da cewa ana Kula da shigar mutane Wanda nan gaba zata Sanya lokacin budewa da rufe Kasuwar domin Kare dukiyoyin al’umma da kuma Hana masu aikata badala a cikin Kasuwar.
Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar, Alhaji Abba Muhammad Bello, a wata zantawa da yayi da manema labarai a Ofishinsa, inda yace hukumarsa ta sha alwashin kawo wa kasuwar gyara ta bangarori da Dama.Alhaji Abba Bello, Shugaban Hukumar KKMB
Alhaji Abba Muhammad Bello ya Kara da cewa “Wannan ofis sabo ne ba mu jima da shigarsa ba, amma yana daga cikin abubuwan da muka fara cin karo da su a kasuwar Wanda yanzu Idan kuka Shiga Kasuwar zaku ga mun fara Sanya kofofin shige da fice a sassa daban-daban na Kasuwar’
Ya ce, “Kasancewata dan kasuwa lokacin da na zo ni da kaina na zaga kasuwar na ga halin da ake ciki kuma abubuwa ne da ba su yi daidai da tsarin kasuwar ba wanda kuma ba za su haifar wa kasuwar da mai ido ba.
“Za mu dauki matakan gyara ta hanyar da ta dace, Amma abin da za mu fara shi ne mu rage yawan mashigar kasuwar domin haka ne zai sa a samu damar kula da masu shiga da fice, Sannan idan komai ya dai-daita za mu dauki matakin sanya lokacin shiga da fita a kasuwar kamar yadda ake yi a sauran kasuwannin jihar nan”
“Sanya lokacin da za mu yi zai zama bisa la’akari da lokacin kasuwanci, misali idan ana bude kasuwa da karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, to haka zamuyi kuma ya Zama wajibi kowa yabi Dokar saboda ta haka ne zamu rage Yawan rashin tsaro a Kasuwar”
Shugaban Hukumar ta (KKMB) ya sha alwashin sanya kafar wando daya da duk wanda zai kawo wa kasuwar nakasu a harkokin kasuwanci Yana mai cewa ” ba zamu yarda mu zuba ido wadansu baki su zo su kassara kasuwarmu ba; Ba za mu ce ba mu son baki ba, domin ita harkar kasuwanci da bakin ake yi; mun yarda kowa ya zo ya ci arziki, amma kamata ya yi kowa ya tsaya a matsayinsa” a cewarsa.
alhaji Abba Muhammad Bello, ya ci gaba da cewa gwamnatin Jihar Kano tana shirye-shiryen kawo ayyukan ci gaba a kasuwar inda ya bukacesu da su bayar da hadin kai. A cewarsa, “Tun kafin zuwanmu Mai girma Gwamna Dakta Abdullah Umar Ganduje, ya fara gyara kasuwar ta hanyar kawo manyan gine-gine a kasuwar wadanda suka kara mata daraja”
” A yanzu har alfahari mutum yake ya zo da baki ya nuna musu Kasuwar Kwari. Kuma gwamnati tana shirin samar da tituna da magudanun ruwa a cikin kasuwar da wasu karin gine-gine.

Leave a comment