Gobara Ta Yi Sanadiyyar Rasuwar Iyalai A Rigasa  Kaduna

Gobara ta yi sanadiyar mutuwar wata mata mai shayarwa tare da jaririnta da kuma wasu kananan yara guda uku a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Layin ‘Yan Tanki da ke Unguwar Rigasa a yankin karamar hukumar Igabi a jihar ta Kaduna.

Shaidun gani da ido sun ce makwabta sun fasa bandakin gidan domin ceto mutanen, sai dai mijin matar kawai mai suna Sani Yahaya Jumare su ka samu a raye wanda daganan su ka garzaya da shi, Asibiti.

Bayanai sun tabbatar da cewa gobarar wadda aka alakantata da tartsatsin wutar lantarki, ta tashi ne da misalin karfe biyu na dare lokacin da mutanen ke tsaka da bacci.

Dole ne Al’umma su hada kai da hukumar Kashe gobara-Usman Alhaji
Samar da lantarki mai amfani da hasken rana ne kadai zai magance tashin gobara a kasuwanni

Wadanda suka rasa rayuka sun hada da Rukayya wadda ita mai dakin sa da jaririnta mai suna Rilwan da wasu ‘ya’yanta da suka hada da: Rabi’atu ‘yar shekarar biyu da Khadija mai shekaru shida da kuma Hajara ‘yar shekaru bakwai wadda ita ‘Ya’ ce ga kanwar mai gidan.

Leave a comment