Sabo Nanono Ya Kunyata Manoma – Kungiyar Masu Noman Zuma

Daga Nasiru Salisu, Kano

Kungiyar masu noman zuma ta kasa ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce daya daga cikin mambobinta wato ministan harkokin noma, Alhaji Sabo Nanono, ya gaza taimakawa kungiyar wajen bunkasa sana’ar noman zuma a kasar nan.

Shugaban kungiyar Kwamared Salisu Adamu Giginyu ne ya bayyana haka yayin zantawa da tashar freedom rediyo.

Ya ce, tun farko sun zaci cewa, tunda daya daga cikin mambobin kungiyar ya samu nasarar zama ministan harkokin noma, to kakarsu ta yanke tsaka, domin kuwa tarin matsaloli da masu noman zuma ke fama da shi a kasar nan, zai zo karshe, amma abin mamaki sai gashi lamarin ba haka yake ba.

‘‘Mun sha yunkurin neman ganawa da Sabo Nanono a lokuta da dama a nan Kano da Abuja, amma lamarin ya citura’’ inji Salisu Adamu Giginyu.

‘‘Muna da tarin matsaloli da dama da ke addabar mu, wanda ya kamata a ce, gwamnati ta shige mana gaba domin dakile su amma kullum lamarin ya ki ci ya ki cinyewa’’-Salisu Adamu Ginginyu.

Shugaban kungiyar masu noman zuman na kasa ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta sanya masu noman zuma cikin kasafin kudin bana amma ya zuwa yanzu ba su san halin da ake ciki ba, saboda hanya daya da za su samu su san ko ina aka kwana kan ayyukan da za a gudanar da ya shafesu, shine ta hanyar ganawa da ministan.

Dan kungiyar mu Alhaji Sabo Nanono, ya rufe duk wata kofar ganawa da shi, inji kungiyar masu noman zuma.

Leave a comment