Dokar Hana Yin Sallar Jam’i A Masallatai Tana Nan Daram- Ganduje

Daga Nasiru Salisu,Kano

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya Kara tabbatar da cewa Dokar Hana Yin Sallar Jam’i A Masallatai Tana Nan Daram-a fadin jihar Domin ganin an dakile yaduwar cutar korona a jihar.

Ganduje yace Duk da cewa yanzu ana cikin watan Ramadana ne Amma Babu Wani abin da zasu iya na bayar da damar gudanar da Sallar Jam’i A Masallatai musamman ganin yadda cutar korona take Kara yaduwa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a Wani taro da yayi da sarakunan gargajiya da Jami’an kiwon lafiya da Kuma kwamitin kar ta kwana na Gwamnatin tatayya akan yaki da cutar korona,Wanda ya gudana a fadar Gwamnatin jihar.

Ganduje,ya bukaci sarakunan da Su taimaka wajen wayar da Kan al’umma dangane da illar Dake tattare da cutar korona, Wanda rage cunkuso Yana daga Yana daga cikin matakan dakile yaduwar cutar.

A nasa jawabin, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Wanda yayi Magana a madadin sauran sarakunan, yayi alkawarin ci gaba da bawa Gwamnatin jihar goyon bayan da suka kamata Domin ganin an dakile yaduwar cutar a jihar Kano Baki daya. Yace sun gamsu da irin matakan da Gwamna Ganduje yake dauka na dakile yaduwar cutar.

Sai wakilinmu ya ruwaito mana cewa da yawan Masallatai a jihar sunyi watsi da Dokar Gwamnatin na Hana Yin Sallar Jam’i inda wasunsu suke ci gaba da gudanar da sallolin guda biyar a kullum.

Sarakunan da suka halarci Taron sun hada Sarkin Bicci da Gaya da na Karaye.

Leave a comment