Shugaba Buhari Ya Nada Gambari A Matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadarsa

Shugaba kasa Muhamamdu Buhari, ya nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa, don maye gurbin Abba Kyari da ya mutu cikin watan jiya sakamakon fama da cutar korona.

Rahotanni sun ruwaito sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha na sanar da nadin na Farfesa Gambari yayin taron Majalisar zartaswa da ke gudana a jiya Laraba.

Farfesa Ibrahim Gambari dan asalin garin Ilorin a jihar Kwara ya rike mukamin ministan harkokin wajen Nijeriya a lokacin mulkin Sojan shugaba mai ci Muhammadu Buhari tsakanin shekarar 1984 zuwa 1985.

Leave a comment