An Samu Jariri Mai Dauke Da Cutar Korona A Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an samu jariri Dan wata hudu Mai dauke da cutar korona a jihar.

Gwamnatin tace jinjirin Yana daga cikin sabbin Masu dauke da cutar guda 20 wadanda aka samu a kananan hukumomi Tara a jihar, wadanda saka hada Kaduna ta Arewa da Chikun da Igabi da Giwa da Kuma Kananan hukumomin Zariya da Makarfi da Soba da Sabon Gari.
Kwamishiniyar Ma’aikatan lafiya na jihar Amina Baloni, itace ta bayyana haka a Wani Sako da ta wallafa a shafinta na “Twitter” inda tace ana samun Masu kamuwa da Cutar ne sakamakon bijirewa Dokar Zaman gida da Kuma wadanda basa bin dokokin rigakafin kamuwa da Cutar.
Hakazalika, tace jinjirin ya kamu da cutar ne bayan sun shigo Kano zuwa Kaduna Wanda yanzu an dauki gwajin iyayen jinjirin Domin sannin matsayinsu akan cutar.

Leave a comment