RASHIN TSARO: Matasa A Katsina Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Daga Safara’u Iliyasu,Katsina
Biyo bayan barazanar rashin Tsaro a jihar Katsina, Wasu matasa a karamar hukumar Jibia dake Katsina sun gudanar da zanga-zanga a yau, inda suka tare babbar hanyar motar dake zuwa Maradi dake Jamhuriyar Nijar, domin bayyana bacin ransu da yadda gwamnati ta kauda kai ‘yan bindiiga na cigaba da hallaka su.

Daruruwan matasan da suka fito daga kauyen Daddara da kauyukan dake makotaka dasu, sun fara zanga zangar ce tun da misalin karfe 8 na safiyar asabar inda suka yi amfani da itace da tsoffin tayun mota wajen cinna wuta akan hanyar, abinda ya tilasta dakatar da zirga zirga.

Bayanai sun ce saida shugabannin al’umma da kuma ‘yan sanda suka lallashi matasan da rana kafin suka yi hakuri suka janye.

Shugaban kungiyar ci gaban ‘Daddara’ Halilu Buhari ya shaidawa Manema labarai cewar sun gaji da yadda ‘yan bindigar ke cigaba da kashe musu mutane da kuma sace dukiyoyinsu.

Buhari yace kwanaki biyu da suka gabata ‘Yan bindigar sun shiga wani kauye da ake kira ‘Yan Gayya, inda suka ci zarafin mata da dama, yayinda suka kuma shiga kauyen Zamdam inda suka yi ta harba na’ura mai fashewa, kafin jama’ar garin suyi kukan kura su kore su.

Al’ummar Jihar Katsina sun dade suna korafi kan irin ukubar da suka samu kansu dangane da hare-haren wadannan ‘yan bindiga wadanda suke cin karensu babu babbaka.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi nasarar tarwatsa mutane a kananan hukumomi da dama, abinda ya sa wasu ‘yan jihar ke sukar gwamnatin tarayya kan yadda tayi watsi da al’amarinsu wajen samar musu da tsaron da ya dace.

Leave a comment