BABBAR SALLA: Matawalle Ya Raba Raguna 550 Da Shanu 132 Ga Malaman Jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya raba raguna 550 ga malaman Addini da limaman jihar domin layya na babban sallar.

Baya ga raguna 550, Matawalle ya raba shanu guda 132 domin yanka su a ranar jajiberin sallah.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar lamuran Addini na jihar Dakta Tukur Sani Jangebe , a zantawarsa da manema labarai a Gusau.

” Mu a jihar Zamfara Gwamna Matawalle ya baya wasa da taimakawa marasa karfi da malaman Addini, Hakan na daga cikin abin da ya sa a gaba” inji shi.

Dakta Jangebe, ya zasu tabbatar da cewa ragunan da shanun an Raba su yadda ya Kamata a daukacin kananan hukumomin jihar kamar yadda aka tsara.

Hakazalika, yace gwamnatin ta bayar da a gudanar da sallar Idi a Masallatan juma’a tare da bin Dokokin hukumomin lafiya domin kaucewa yaduwar cutar Korona.

Idan ba a manta ba a lokacin karamin sallah ya taimaka wa marasa karfi sama da mutum 100,000 da kayan sallah, abinci da kayan masarufi.

Leave a comment