KORONA: Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Soke Bukukuwan Salla

Gwamnatin jihar Jigawa dake Arewacin Nijeriya ta bayar da umarnin Hana bukukuwan Bababar sallah wanda za’a yi a ranar juma’a mai zuwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Dakta Abba Zakari Umar, yayin taro da Masu da tsaki a jihar.

Dakta Abba Umar, wanda kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar cutar Korona a jihar, yace gwamnatin ta dauki matakan Hana duk wani biki bayan kammala sallar Idi domin kaucewa yaduwar cutar Korona.

Kwamishinan yace ya zama wajibi ga Masu masallacin Idi da su tabbatar da sun Sanya takunkumin rufe fuska da kuma bada tazara yayin gudanar da sallar Idin wanda hakan Yana da cikin matakan Hana yaduwar cutar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Jigawa ta himmatu wajen daukar matakan dakile yaduwar cutar.

Leave a comment