TSARO: Buhari Ya Sayo Jirgin Yaki Daga Kasar Rasha

Jirgin dakon kaya daga Kasar Rasha ya sauka lafiya a filin jirgin sama na sansanin sojojin saman Nijeriya dake garin Makurdi a jihar Benue.

Jirgin ya sauke wani jirgin yaki na zamani mai saukar ungulu kirar Mi-28NE wanda gwamnatin shugaba Buhari ta saya daga Kasar Rasha domin a yaki ‘yan ta’adda.

Wannan shine jirgin yaki mai saukar ungulu da Nijeriya ta mallaka wanda babu irin sa a kyau da tsada, gudu da kuma gaggawan kaiwa hari

Leave a comment