BATA SUNA: Sanata Mandiya Ya Maka Mahadi Shehu A Kotu

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kudancin Katsina A Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Bello Mandiya ya Maka Mahadi Shehu a kotu bisa zargin Bata suna.

Sanata Bello Mandiya, ya shigar da karar Bata suna a babban kotu dake jihar Katsina bisa abin da ya kira Bata suna wanda Dan kasuwa a jihar Kaduna Mahadi Shehu yayi Masa.

Sanata Mandiya, wanda shine shugaban ma’aikata a fadar Gwamnatin jihar Katsina, ya bayyanawa manema labarai a Abuja cewa, Mahadi Shehu ya zargi Shi ( Mandiya) da hannu wajen karkatar da kudadan Tsaro a jihar, inda yace zargin bashi da tushe ballantana makama.

Mandiya yace kotu ce zata bi Masa hakkinsa, akan zargin da Mahadi yayi Masa na Bata suna a idan Duniya.

A kwanan baya ne Mahadi Shehu, ya zargi Sanata Mandiya da hannu wajen karkatar da kudin Tsaro na jihar har naira Miliyan 500 lokacin da yake shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina.

Sai Dai an ruwaito Mandiya Yana karyata zargin inda yace bashi da tushe, lamarin da ya Sanya ya Maka mahadi Shehu a kotu domin bi Masa hakkinsa na Bata suna.

Mahadi Shehu, Babban Dan kasuwa ne kuma haifaffen jihar Katsina mazauni jihar Kaduna, ya Dade Yana caccakar gwamnatin jihar Katsina bisa zargin aikata ba daidai ba dukiyar Al’ummar jihar.

Leave a comment