Muna Daukar Matakan Tsaro A Tashar Kwanar Dawaki- Danladi

Daga Mohammed Auwal

Kungiyar ma’aikatan Sufuri ta Kasa (RTEAN) reshen Kwanar Dawaki Dake jihar Kano, ta bayyana irin matakan da take dauka na magance matsalar Tsaro a tashar domin kare Lafiya da dukiyar Fasinjoji.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar Alhaji Danladi Baba, a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake Kwanar Dawaki inda yace suna daukar matakan tantance Fasinjoji da kayansu.

Alhaji Danladi, wanda shine Ma’ajin kungiyar ta jihar Kano, ya bayyana cewa tuni suka fara daukar matakan tantance Fasinjoji Kamin su hau mota wanda ta haka ne zasu iya Gano Bata gari masu shigar burtu a tashar.

Akan hakan yace, har ya zuwa yanzu babu wani batagari da aka kama a tashar bisa irin matakan Tsaro da suke dauka a tashar.

Alhaji Danladi Baba, wanda kuma shine Mai Anguwa Tamburawa, ya Yaba da kokarin gwamnatin jihar Kano karkashen jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na daukar matakan Tsaro a jihar, inda yace jihar Kano Allah Yana kareta da fadawa cikin duk Wata matsalar Tsaro ko annoba a fadin jihar.

Hakazalika, ya jinjinawa kokarin kwamishinan ‘yan Sandbar jihar Kano, Abu Sani, na samar da yanayin mai kyau na inganta Tsaro a jihar, Yana mai cewa al’ ummar Kano suna Jin dadin ayyukan kwamishinan.

Akan hakan, shugaban ya bukaci daukacin Al’ummar jihar masu mu’amala da tashoshinsu su ci gaba da Bawa kungiyar goyon bayan da suka Kamata domin kare rayuka da dukiyar su a tashar.

Leave a comment