Gwamna Badaru Ya Kori Shugaban Jamiyyar APC Na Jihar Jigawa

Daga Mohammed Auwal, Kano

Gwamnan jihar Jagawa Mohammed Badaru Abubakar, ya kori shugaban jami’iyyar APC na jihar Alhaji Habibu Sara, daga kan kujerar shugabancin jami’iyyar bisa abin da ya kira da zagon kasa da shugaban yake yiwa gwamnatinsa.

A wani taron masu ruwa da tsakin jami’iyyar da gwamnan yayi a fadan gwamnatin jihar dake Dutsw, yace gwamnatinsa Ba zata aminta da duk wani wanda yake yi Mata zagon kasa ba.

Jim kadan bayan kammala taron ne Gwamnan ya sanar da cewa jami’iyyar APC ta jihar ta kori Alhaji Habibu Sara daga shugabancin jami’iyyar.

Wakilinmu, ya ruwaito mana cewa ya zuwa lokacin aiko da wannan rahoton, jami’an ‘yan Sanda sunyi wa hedikwatar ja’ iyyar kawanya bisa shirin ko ta kwana.

A zantawarsa da manema labarai Alhaji Habibu Sara, yace har yanzu shine shugaban jami’iyyar na jihar, Yana mai cewa babu wanda ya sauke shi daga kan shugabancin ta.

Habibu Sara, yace “abin da na Sani shine akwai wasu mutane da Gwamnan baya son muna Tarayya dasu saboda Wai basa tare da gwamnatinsa amma ni asani na ‘yan Jamiyyar APC ne su saboda haka ya zama dole Wai Sai na rabu dasu, ni kuma bazan iya ba. Ikararin an koreni daga shugabancin Jamiyyar ban Sani ba domin har yanzu nine shugaban ta na jihar Jigawa “inji shi.

Leave a comment