Barcelona Zata Rage Albashin Messi

Shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu zai bukaci Lionel Messi da ya amince da matakin zabtare albashinsa kamar yadda jaridar Deportes Cuatro hta rawaito.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mujallar Forbes ta bayyana Messi a matsayin dan wasan kwallon da ya fi samunn kudin shiga a bana.

Forbes ta kiyasta cewa Messi ya samu Dala miliyan 126 a shekara guda, yayin da Cristiano Ronaldo na Juventus ke matsayi na biyu da Dala miliyan 117.

Neymar na PSG na matsayi na uku da zunzurutun Dala miliyan 96 da ya samu a cikin shekara guda.

Sai Kylian Mbappe na PSG da ke matsayi na hudu da Dala miliyan 42, yayin da Mohd. Salah na Liverpool ke matsayi na biyar da Dala miliyan 37

Leave a comment