Zamu Samar Da Wadataccen Taki Ga Nanoma- Cewar Kamfanin Takin Continental

Daga Shehu Yahaya

A Kokarinsa na samar da takin zamani mai inganci kuma mai saukin farashi ga dauka in manoman kasar nan, Kamfanin samar da Takin zamani na (Continental Fertilizer and Chemicals) dake jihar Kano A Arewacin Nijeriya, ya yi alkawarin samar da Taki wadatacce a daminan bana ga manoma a fadin kasar nan baki baya.

Kamfanin na Continental ya bada tabbacin cewa zai samar da takin wanda zai zama mai inganci daidai da yanayin kasar noman da ake da ita, bisa farashi mai sauki da kuma inganci tare da wadatar samuwar takin a duk lokacin bukatarsa daga Kano zuwa wasu jihohi dake fadin Nijeriya.

A zantarwasa da manema labarai Jim Kadan bayan kungiyar ‘yan jarida ta Arewa ta karrama kamfanin da lambar Yabo, Babban shugaban kamfanin Na Continental Alhaji Ibrahim Saulawa, ya bayyana cewa kamfaninsu ya kudiri aniyar samar da takin zamani mai inganci da Nagarta wanda duk manomin da yayi amfani dashi zai samu amfani mai yawa.
Acewarsa kamfaninsu zai samar da aikin yi ga matasa Masa masu wadanda suke aiki kai tsaye da kamfanin zuwa ‘yan sarin kayanssu da kuma ‘yan talla, wanda mafiyawan wadanda zasu amfana manoma ne, da matasa masu neman sana’a.
Alhaji Ibrahim Saulawa, ya godewa ‘yan jaridu da suka karrama kamfanin bisa irin gudunmuwa da yake bayarwa na bunkasa aikin gona a kasar nan.

Leave a comment