Gwamnatin Kaduna Ta bada Umarnin Bude Makarantu A Fadin Jihar

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta kammala Shirinta na bude makarantu a ranar 18 da 19 ga wannan watan Oktoba.

Kwamishinan ma’aikatar ilimin Jihar Kaduna Dokta Shehu Usman Muhammad Makarfi shi ya bayyana haka a taron manema labarai da aka yi a cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna jiya Laraba.

Alhaji Shehu Usman Muhammad ya ce dukkan tanajin da ya dace ayi tuni an kammala shi don haka dalibai na makarantun kwana da za su koma domin yin jarabawar wucewa aji na gaba daga aji hudu na babbar sakandare zuwa aji biyar na babbar sakandare sai kuma daliban da za su shiga aji uku a babbar sakandare ana umartarsu su koma a ranar 18 ga masu makarantar kwana

Sai kuma dalibai na makarantun jeka ka dawo suma su koma a ranar 19 ga wannan watan domin masu kokarin wucewa aji na gaba su samu damar rubuta jarabawa.

Kwamishinan ya bayyana cewa haka abin yake a batun makarantun gaba da sakandare na jami’ar Jihar Kaduna, kwalejin ilimi ta gidan waya da kuma Nuhu Bamalli da ke Zariya, amma su an umarce su da su yi tsarin karantar da dalibai ta hanyar yin amfani da yanar Gizo da kuma hadawa da karantar da dalibai ta hanyar da aka saba domin rage cinkoson dalibai a wuri daya ta yadda dalibai za su iya yin darasinsu suna cikin gidajensu.

Kwamishinan ya ce ana son dalibai Ashirin ne a kowane aji kuma za a yi amfani da tsarin yin karatu na Zango biyu a kowace rana.

” Ta yadda idan dalibai sun zo da safe za su yi karatun Awa hudu zuwa sha biyu na rana sai kuma wadansu su fara daga karfe biyu na rana zuwa biyar na Yamma a kowace rana tare da kiyaye dukkan ka’idojin da aka shimfida.

Ya ci gaba da cewa a makarantun kwana akwai tsarin babbar na’urar auna zafin jikin mutum da dukkan dalibai za su rika wucewa ta cikinta domin tantance zafin jikinsu a koda yaushe.

Sai kuma ruwa da abubuwan wanke hannu da Takunkumin rufe baki da hanci da kuma tsarin samar da tazara a tsakanin al’umma da bin dukkan matakan da ya dace

Kuma duk haka lamarin yake ga makarantu masu zaman kansu sai dai mun yi zama da su mun kuma cimma babu karbar kudin makaranta na tsawon lokacin da ba a yi karatu ba amma za a karbi wani abu na tsarin karantar da dalibai da aka yi ta hanyar amfani da yanar Gizo domin rage kashe kudin aka yi wajen gudanar da irin wannan tsarin karatu.

Kwamishinan ya kuma ce za a ci gaba da komawa makarantun ne sannu a hankali, kuma har makarantun Islamiyya ma ana tattauna yadda za a koma karatu

Ya kara da cewa akwai Makarantu 120 da suke bukatar gyara a fadin Jihar Kaduna kuma tuni aka duba su sosai har an san za su lashe kudi naira miliyan dari 400 domin gyara su kuma tuni Gwamna ya amince da hakan.

Sai kwamishinan ilimin ya kara da cewa koda batun kudin ya wuce hakan Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, a shirye yake ya kashe kudi ko nawa ne domin ilimi ya ci gaba a duk fadin Jihar baki daya.

“Muna kira ga iyayen yara da su sayawa yayansu wani karin Takunkumin rufe baki da hanci domin dalibai su samu sukunin yin amfani da wani idan sun wanke wanda suke amfani da shi”.

Leave a comment