NLC Tayi Juyayin Rashin Shugaban Kungiyar NULGE Na Kasa

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

MAJALISAR Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen Jihar Kaduna ta bayyana rasuwar ma’ajin Kungiyar ta Kasa kuma Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi (Kwamared Ibrahim Khaleel Abdulkadir) a matsayin babban rashi ga kungiyar kwadago, danginsa da Kasar baki daya.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Kwamared Ayuba Magaji Suleiman da Sakatariyar Kungiyar Kwamared Christiana John Bawa suna jajantawa Shugaban CWC, mambobin NEC, NLC, danginsa NULGE, Iyalensa, abokai da kuma makusantan shi kan rasuwar sa.

Marigayi Kwamared Ibrahim Khaleel, Abdulkadir Ma’ajin NLC ta kasa kuma Shugaban Kungiyar Ma’akatan Kananan Hukumomi

Sanarwar ta bayyana marigayi Ma’ajin NLC kuma Shugaban NULGE a matsayin ginshiƙi a gwagwarmayar, wanda yanzu mutuwarsa ta haifarda gurbi wanda zai yi matukar wahala a cika shi.

Sanarwar ta ce marigayi Ibrahim Khaleel Abdulkadir babban jagora ne wanda ya ba da gudummawa ga jin dadin ma’aikatan kananan hukumomi kuma ya yi aiki da kungiyar kwadagon Najeriya da kwazo da jajircewa.

Kungiyar tana rokon Allah ya gafarta masa kurakuransa kuma Yasa aljanna ce makomarsa ta karshe.

Marigayi Kwamared Ibrahim Khaleel ya mutu a Asibitin Kasa da ke Abuja, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Shugaban NULGE na Kano, Abdullahi Muhammad Gwarzo wanda ya tabbatar da mutuwar a daren ranar Laraba, ya ce za a binne mamacin a Wudil, karamar hukumar Jihar Kano da yammacin Alhamis.

Ibrahim Khaleel, dan asalin Wudil ne dake karamar hukumar Wudil a jihar Kano.

An sake zabarsa a matsayin Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) da kuma Ma’ajin Kungiyar Kwadago ta kasa na, NLC

Leave a comment