Ba Zamu Lamunci Masu Fakewa Da Zanga-Zanga Suna Tada Hankalin Al’umma Ba- Inji Gwamnonin Arewa

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriyi 19 ta bayyana cewa ba za ta yadda da irin barnar da wasu keyi da sunan zanga-zanga ba, lamarin da ya haddasa Asarar rayuka da dukiyoyin Al’umma ba.

A wani taron gaggawa da kungiyar tayi a jihar Kaduna a jiya Alhamis sun ce ba su ji dadin abun da ke faruwa a wasu sassan Nijeriya ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewan kuma gwamnan Filato Simon Bako Lalong, shi ya yi magana a matsayin gwamnonin baki daya.

Yace abin da su ke bukata shi ne masu zanga zangar su jira su ga abinda gwamnati za ta yi a matakin jihohi da kuma gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa gwamnati ba za ta lamunci yadda wadansu suke fakewa da zanga zangar lumana da matasa su ke yi na neman mafita su tada hankalin al’umma ba.

Gwamnonin Arewan sun yaba da kauracewa zanga-zangar da wadansu matasan Arewa su ka yi sannan kuma su ka ce su na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hasalima, Gwamnonin Sun bayyana cewa suna tuntubar gwamnonin kudancin kasar tare da jinjinawa gwaman jihar Lagos inda lamarin ya fi muni.

Leave a comment