ENDSARS: Gwamnati Zata Yi Amfani Da Bukatun Masu Zanga-Zanga.. Buhari

Biyo Bayan koke-koke da gudanar da zanga-zanga a fadin Nijeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa ‘yan kasar jawabi a kan kisan wasu masu zanga-zanga da ake zargin jami’an rundunar soji da aikatawa yana mai rokon yan kasa su rungumi zaman lafiya.

A jawabin sa ga ‘yan Nijeriya, shugaba muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya zama wajibi ya yi magana da su bayan korafe-korafe da ya samu daga bangarori daban-daban a kan yanayin da ake ciki a kasar da kuma ganawa da ya yi da manyan hafsoshin tsaro yana mai gargadi ga marasa kishin kasa da ke amfani da damar masu zanga-zangar lumana na #ENDSARS domin cimma manufa na daban su gujewa ci gaba da hakan.

Shugaban ya kuma bayyana rashin jin dadi game da rahoton da ya samu a ranar litinin na yin amfani da karfi kan masu zanga-zanga yana mai cewa ‘yan Nijeriya na da yancin gudanar da zanga-zanga kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar sashi na 40 ya tanadar ba tare da takewa sauran ‘yan kasa yancin gudanar da ayyukan su na yau da kullum ba.

Shugaba Buhari ya bayyana damuwa matuka kan rasa rayyuka da dukiyoyi yana mai jan hankanli kasashe makwabta da sauran kasashen duniya su rinka bincike domin gano gaskiyar lamarin dake faruwa kafin su dauki matakai cikin gaggawa a kai inda ya roki matasa masu zanga-zanga su yi hakuri su rungumi zaman lafiya kuma gwamnati zata aiwatar da dukkan bukatun da suka mika

Leave a comment