Mahara Sun Kashe Mutane 13 A Zamfara

Daga Asma’u Abdullahi

Wasu mahara masu satar shanu sun kashe mutane 13 a wani kauye dake jihar Zamfara a ranar Asabar data gabata.

Maharan sun afka wa kauyen Kadamutsa dake karamar hukumar Zurmi ta jihar ne da misalin karfe 3 na rana, kuma suka ci Karen su ba babbaka na fiye da sa’o’i 2, kamar yadda wata majiya a yankin ta shaida wa RFI Hausa.

Majiyar ta ce maharan sun kwashe wannan tsawon lokaci suna dibar shanu da sauran dabbobi tare da harbin mutane ba tare da wani dauki daga jami’an tsaro ba.

Majiyar ta ci gaba da cewa wasu daga cikin mutane 13 da ‘yan bindigar suka kashe ‘yan banga ne da suka kai gudummawa daga kauyukan dake makwaftaka da kauyen Kadamutsa.

Wannan harin na zuwa ne duk da sulhun da gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce ta yi da ‘yan bindigar.

Al’ummomi a yankuna da daman a arewacin Najeriya sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon kisan gillar da wadannan ‘yan bindida suke musu a kai a kai.

Ko a cikin makon da ya gabata, an samu rahotanni akan hare haren ‘yan bindiga a kauyuka kusan biyar na jihar Zamfara.

Wannan lamari ya hana al’ummomin da abin ya shafa yin noma saboda tsoron zuwa gonakinsu, abin da ya sa manazarta ke ganin zai haddasa matsalar abinci a shekara mai kamawa idan ba gwamnati ta kai dauki ba.

Leave a comment