Gwamnatin Nijeriya Zata Biya ASUU Naira Biliyan 65


Gwamnatin Nijeriya ta sauya matsayi kan jayeyyar da take yi da kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU kan batun biyan kudaden alawus -alawus din malaman, inda tayi tayin bada naira biliyan 65, domin biyan wasu bukatun nasu.

Ministan kwadago da ayyukan yi Dakta Chris Ngige ne ya bayyana matakin na gwamnati yayin ganawa da kungiyar malaman a ranar Jumma’a.

Ministan wanda ya bayyana tattaunawar a matsayin mai muhimmaci, ganin yadda dalibai suka kasance babu karatu tsawon watanni, yace, gwamnati ta amince ta biya malaman tsohon tsarin albashi maimakon sabon tsarin IPPIS da su ke jayayya akai.

Leave a comment