Gwamnatin Nijeriya Ta Kaddamar Da Shirin Tallafawa Matan Karkara Da Jari

Minista Sadiya Umar

Daga Husna Hassan

Shirin nan na Gwamnatin Tarayya na raba agajin tsabar kuɗi ga matan karkara, wato ‘Cash Grant for Rural Women’, yanzu ya fara aiki a yankin kudu-maso-gabashin ƙasar nan.

Hakan ya biyo bayan ƙaddamar da shirin wanda Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi a Jihar Ebonyi a ranar Alhamis da ta gabata.

A wajen taron ƙaddamarwar wanda aka yi a tsohon Gidan Gwamnati da ke garin Abakaliki, ministar ta shawarci matan da aka raba wa kuɗin da su kashe wannan biya sau ɗaya na N20,000 ga kowaccen su ta hanya mai kyau, musamman wajen ƙara jarin ƙananan sana’o’in da su ke da su.

Ta bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ce ta kafa shirin don ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa a cikin shekaru goma.

Ta ce: “Saƙon mu a gare su shi ne su yi amfani da wannan kuɗi ta hanya mai kyau wajen fara ƙananan sana’o’i ta yadda cikin yardar Allah wannan kuɗi zai ruɓanya yawan sa har su samu damar kula da kan su da iyalan su.

“Mu na fatan gwamnatin Jihar Ebonyi za ta taimaki waɗannan matan da shawarwari tare da goyon baya da sanin makamar aiki, ta ci gaba da ɗora su a kan hanyar gudanar da sana’ar da kowace mace ta zaɓa.”

Cikin nasa jawabin, Gwamnan Jihar Ebonyi, Injiniya David Umahi, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda wannan shirin wanda ya ce zai taimaka gaya wajen rage wahalhalun da matan karkara su ke ciki a jihar.

Gwamna Umahi, wanda Mataimakin Gwamna Eric Kelechi Igwe ya wakilta a taron, ya bayyana ziyarar da ministar ta kai da cewa ta zo a kan kari, sannan ya yi alƙawarin cewa matan za su fara cin moriyar kuɗin jarin da aka ba su nan ba da jimawa ba.

Ya ce, “Wannan babbar rana ce domin rana ce kuma da mutanen Ebonyi su ka tashi daga ɓangaren hagu zuwa na dama. Babu wata gwamnati da ta taɓa yi wa mutanen Ebonyi irin wannan.

“Na gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da Minista Sadiya Umar Farouq saboda fito da waɗannan tsare-tsare na cigaban ƙasa.

“Mata mutane ne masu himma. In da maza ne su ka samu wannan kuɗin, washegari sai ka ji za su yi aure da kuɗin.

“Mata ba su ba maza umarni, to amma su kan tabbatar da cewa akwai abinci a gida. Saboda wannan abin alheri, mu na godiya, kuma za mu ci gaba da kawo ƙoƙon barar mu.”

Haka kuma mataimakin gwamnan ya yi kira ga ministar da ta fito da hanyoyin da za a riƙa sa ido kan shirin don auna yadda matan ke ci gaba da amfana da shi a kasuwancin su ko kuma duk abin da su ka yi da kuɗin jarin.

Ana sa ran sama da mata 200 daga ƙananan hukumomi 13 da ke Jihar Ebonyi ne za su amfana daga wannan shiri na Gwamnatin Tarayya mai suna ‘Cash Grant for Rural Women’.

Leave a comment