Ba mu Karbi Tallafin Kudin Korona Ba -Minista Sadiya

Daga Husna Hassan

Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta ce ma’aikatar ta ba ta amshi gudummawa ko ta sisi, a nan cikin gida da kuma kasashen waje, da sunan tallafin korana ba.

Sadiya ta bayyana haka a lokacin da ta ke kare kasafin ma’aikatar ta na 2021, a gaban kwamitin Majalisar Tarayya.

Ministar ta yi wannan ikirari bayan Najeriya ta karbi bilyoyin kudade a matsayin kudaden gudummawar tallafi da yaki da cutar korona, daga hannun kamfanoni, bankuna da daidaikun jama’a.

Sadiya ta ce ko sisi ba a bai wa ma’aikatar ta ba a cikin kudaden wadanda wasu daidaikun jama’a da kamfanoni su ka bayar gudummawa.

Ya zuwa karshen watan Afrilu, kudaden da Najeriya ta tara daga gudummawa, sun kai naira bilyan 27.160.

Ta ce amma ba a bai wa ma’aikatar ta ko sisi ba.

Wasu da su ka bada gudummawa mai tsoka sun hada da Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu, Segun Agbaje (GTB), Tony Elumelu (UBA), Oba Otudeko (First Bank), Jim Ovia (Zenith Bank), Herbert Wigwe (Access Bank) da kuma Femi Otedola (APD).

Da ta ke magana a kan rabon tallafi, cewa ta yi ma’aikatar ta abinci kawai ta karba daga hannun gwamnatin tarayya.

“Ba mu karbi ko sisi ba, amma mun karbi kayan abinci.” Inji Minista Sadiya.

Ta kara da cewa baya ga kasafin ma’aikatar, ba su karbi karin kudi ko naira daya daga hannun gwamnatin tarayya da sunan kudaden tallafin raba wa jama’a ba.

Sadiya ta kara da cewa daga cikin kasafin ma’aikatar, kashi 50 kadai ta iya karba daga hannun gwamnatin tarayya.

Leave a comment