Daga Mohammad A. Mohammad
A Kokarinsa na samar da takin zamani mai inganci kuma mai saukin farashi ga dauka in manoman kasar nan, Kamfanin samar da Takin zamani na Alelawa Fertilizer and Chemicals dake jihar Sakkwato A Arewacin Nijeriya, ya yi alkawarin samar da Taki wadatacce ga manoma a fadin kasar nan baki baya.
Kamfanin na Alelawa, ya bada tabbacin cewa zai samar da taki wanda zai zama mai inganci daidai da yanayin kasar noman da ake da ita, bisa farashi mai sauki da kuma inganci tare da wadatar da takin a duk lokacin bukatarsa ta taso zuwa wasu jihohi dake fadin Nijeriya.
Akan hakan, shugaban na kamfanin Alelawa, ya jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari, akan inganta harkokin noma musamman na samar da shirin samar da Takin zama na gwamnati Wanda ake kira ( Presidential fertilizer Initiatives). Shirin da yake taimakawa manoma da takin zamani mai inganci akan farashi mai sauki.
Yace shirin ya taimaka waje inganta harkokin noma a fadin kasar Nan baki daya.