Gwamnatin jihar Sakkwato Zata Kafa Hukumar Hisba-inji Kwamishinan Addinin Musulumci

Hon. Abdullahi Maigwandu

Daga Mohammad. A Mohammad

Gwamnatin jihar Sakkwato ta Kammala shirinta na kafa hukumar Hisba ta jihar domin ganin an Kara samar da yanayi mai kyau na Kula da tarbiyyar al’ummar jihar bisa tsari da dokokin addinin Islama.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar Lamuran addinin musulunci ta jihar Hon. Abdullahi Maigwandu, a Wata zantawa da yayi da manema a labari a ofishinsa.
Kwamishinan yace tuni kwamitin da gwamnan ya kafa akan tsara yadda hukumar Hisba zata kasance ya miki rahotonsa.
Hon. Abdullahi Maigwandu, ya ci gaba cewa “Mai girma gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi rahoton Kwamitin daya kafa akan aikin Hisba a jihar karkashin jagorancin mai girma Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali Junaidu tare da mambobin wannan kwamitin wadanda suka hada da wakilan ja’mian tsaro daga kowane bangare”

Gwamna Tambuwal tare da Wazirin Sakkwato

“Akwai Manyan Malaman addini da sauran su Wadanda Sun gabatar da rahoton wannan kwamitin ga maigirma gwamna a fadar gwamnatin jihar” inji shi.
Idan aka kafa hukumar ta hisba zata kasance karkashin kulawar ma’aikatar lamuran Addinin musulunci ta jihar .
Kwamishinan ya kuma bada tabbacin cewa Nan bada jimawa ba gwamnati zatayi duba tare da aiwatar akan rahoroton na kafa hukumar Hizba a jihar domin kara ingantuwar aikinta.
Yayin karbar wannan rahoton gwamna Tambuwal ya bayyana jin dadin sa tare da yabawa ga dukkanin ‘yan wannan kwamitin bisa hazaka da kokarin da sukayi na sauke nauyin da gwamnati ta Dora masu domin samar da hanyar da za’a inganta aikin Hizba a jihar Sakkwato.

Leave a comment