Muna Iya Bakin Kokarinmu Wajen Magance Matsalar Tsaro- Gwamnonin Arewa

Daga Shehu Yahaya, kaduna

A daidai lokacin Da matsalar rashin tsaro yake kara ta’azzara a jihohin Arewacin Kasar nan. kungiyar gwamnonin Arewa tare da majalisar sarakunan yankin na gudanar da muhimmin taro a Kaduna domin tattarawa a kan sha’anin tabarbarewar tsaro, da sauran batuntuka da suka shafi ci gaban yankin domin nemo mafita da nufin shawo kan lamurran .

Da yake gabatar da sakon shugaban kasa, sakataren gwamnatin tarayya Farfesa Suleiman Gambari ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da matsayin gwamnatin shi na tsare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gudanar da ayyuka domin inganta rayuwar al’umna da ci gaban kasa wanda ya kunshi fannoni daban dabam .

Farfesa Ibrahim Gambari haka ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da kokarin gwamnonin a bisa da fadi tashin da suke yi domin ganin an kyautata sha’anin tsaro a Jihohin su .

Daga nan sai ya bukaci taron da ya tabo muhimnan batuntuka wadanda zasu taimaka wajen magance matsalolin da suke hana ruwa gudu wajen ci gaban yankin da kasa baki daya .

Tun da farko a jawabin shi na maraba, gwamna Mallam Nasiru Ahmed El-Rufa’i bayan ya yi wa manyan baki maraba sai ya ce ta bangaren tabarbarewar tsaro takwarorin shi na iyakan bakin kokarin su na tabbatar da cewa an kawo karshen wannan lamarin da ya ta’azzara .

Haka a jawabin shi, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Jihar Filato Mista Simon Lalong, ya fara da yin maraba ga mahalarta taron sa’annan ya ce a makon da ya gabata sun yi taro a nan Kaduna tare da shugabannin rundunar dajoji, da sauran masu fada aji a yankin Arewa maso yamma inda suka tattauna a kan batun tsaro da sauran matsalolin da suka addabi yankin inda suka yanke shawarar sake zama na musamman domin ci gaba da tattaunawa tare da fitar da matsaya na yadda za’a sami saukin al’amura .

Gwamna Simon Lalong har ila yau ya ce akwai kwamitoci daban dabam da aka kafa wadanda shugabannin kwamitocin za su yi bayanin irin nasaririn da suka samu wanda taron zai duba kuma ya samar da matsaya guda .

Shi ma mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce ya zama waJibi su jinjina wa gwamnonin a bisa ga kokarin da suke yi na shawo kan matsalolin rashin tsaro tare da kara basu kwarin guiwa na ci gaba da daukar matakai domin cimma nasarar da ake nema .

Dangane da batun Almajiranci kuwa ya ce majalisar sarakuna suna yin abin da ya kamata domin magance matsalolin da yake haifarwa .

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kara da cewa rashin isasshen kudi shi ne jawo masu tarnaki wajen gudanar da ayyukan amma ya ce gwamnonin na kokari daidai gwargwado sauran kuma sai a bar wa ubangiji Allah.

Haka shi ma mukaddashin shugaban majalisar wakilai na kasa Rt.Hon. Idris Wase a madadin majalisar tarayyar sun bayyana jin dadin su ga kungiyar gwamnonin Arewa bisa ga kokarin da suke yi na ganin an kyautata sha’anin tsaron rayukan al’umma da ci gaban yankin da kasa baki daya .

Ya ce majalisar za ta ci gaba da ba da goyon baya a kan duk wani shuri da zai kara samar da hadin kan kasa tare da samar da abubuwan da za su kyautata rayuwan al’umma baki daya .

Ana sa ran samun cikakken sakamakon tattaunawar a karshen taron

Leave a comment