Fulani Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne- Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III ya bayyana cewa, Fulani ba ‘yan ta’adda ba ne.A

lhaji Abubakar ya fadi haka ne a birnin Abuja a yayin wata ziyara da ya kai wa Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON.

Sarkin Musulmin ya ce,

Tun da fari ina kan bakata, mu ba ‘yan ta’adda ba ne. Tabbas akwai ‘yan bindiga a cikinmu, amma hakan bai mayar da wata kabila ko kuma daukacin Musulmi miyagu ba. in ji Sarkin Musulmi.

Wannan na zuwa ne a yayin da wasu daga cikin Fulani ke ci gaba da kaddamar da hare-haren bindiga musamman a arewacin Najeriya, inda suke garkuwa da mutane domin karbnar kudin fansa.

Leave a comment