Fasa-Kwauri: Hukumar Kwastam Tayi Babban Kamu A Kaduna

Daga Shehu Yahaya, Kano

Hukumar hana Fasa-kwauri ta kasa shiyyar Arewa (FOU B) Mai hedikwata a jihar Kaduna ta kama kaya nau’uko daban-daban Wanda darajarsu ya haura Naira miliya 66 a cikin kwanaki 14 daga jihohin daban- daban a jihohin Arewa.

Kayan wadanda yawansu ya kai guda 51 iri daban-daban sun haxa guda hudu jarkokin man gyaxa 227 jarkar man Fetur guda 49 Mai nauyin 25kg sai jarkar basin Mai 38 Mai nauyin 25kg da kuma dilar gwanjo guda 67.

Da yake bajekolin kayayyakin a gaban manema Labarai a hedikwatar hukumar, Kwanturolan hukumar na shiyyar, Al- Bashir Hamisu, yace manya daga cikin kamun da suka yi sun haxa da wuqake guda 180 Wanda aka kama a garin Tsafe dake jihar Zamfara da motoci guda 13 xauke da buhun shinkafa ta Waje buhu 592.

Kwanturolan ya ce sun qwace kayan ne cikin kwanaki 14 da suka gabata, yana mai bayyana masu Fasa-qwaurin a matsayin masu yin zagon ƙqasa ga ci gaban tattalin arziƙin qasa.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bawa hukumar tasu haxin kai wajen ganin an kakkave masu ire-iren waxannan laifuka.

“Ina kira ga jama’a da su ci gaba da ba mu muhimman bayanai cikin sirri da za su taimaka wajen ganin an kawo qarshen ayyukan masu Fasa-qwaurin,” inji kwaturolan.

Hamisu, yace ofishinsa yana kula da jihohi 7 na Arewa da wasu jihohi guda Biyu na shiyyar Arewa ta tsakiya da kuma Babban Birnin tarayya ābuja Wanda kuma kayan da suka kama an kama su ne a tsakanin jihohin.

Leave a comment