Sayar Da Matatun Man Fetur Alherine Ga Nijeriya- inji Usmaniyya

Daga Shehu Yahaya, kaduna
Tsohon shugaban kungiyar Dillalan man Fetur ta qasa (IPMAN) reshen jihar Kaduna Alhaji Abubakar Shariff Usmaniyya, ya bayyana cewa sayar Da Matatun Man Fetur na kasar nan da gwamnatin tarayya zatayi zai zama alheri ne ga ci gaban tattalin arzikin qasar baki xada.
Alhaji Abubakar Sharif, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema Labarai Inda yace babu wani alfanu da gwamnatin tarayya take samu a matatun illa tafka asara na maqudan kuxaxe Wanda sayar dasu shine mafita.
Alhaji Sharif Usmaniyya, Wanda xan kwamitin amintattune na kamfanin hada-hadar man Fetur na (NIPCO) ya qara da cewa duba da irin xawainiya da gwamnatin tarayya takeyi na gyara Matatun Man amma har yanzu sun kasa zama da kansu , a cewarsa babu abin da suke Kawo wa qasar illar asara kawai.
“Xata daga cikin abubuwan da ya sanya gwamnati zata sayar Da matatun tace akwai batun samawa matasa aikinyi Wanda babu maganar sai Xan wane ko daga wurin wane kake , cancanta kawai za’abi saboda ni na gamsu da wannan qudiri na shugaban qasa akan sayar Da Matatun Man Fetur kuma muna ganin yin hakan zai zama alheri ne Ga ci gaban tattalin arzikin , qasar baki xada ” inji shi.
Akan hakan ya jinjinawa gwamnatin tarayya Akan qudirinta na sayar Da matatun yana Mai cewa “duk abin da kaji gwamnati tace data sayar dashi to Bata samun riba ne kuma tana ganin hakan shine mafita Ga ci gaban qasar”
Shugaban ya bada misalin matatar man Fetur ta Kaduna wacce an dade Ana kashe qudade wajen gyara ta amma har yanzu ta kasa tsayawa da kanta , a cewarsa, idan aka gyara yau gobe sai ta lalace Wanda hakan asara ne ga gwamnati.

Leave a comment