An Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Kaduna Da Kungiyar kwadago

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce an cimma matsaya dangane da takaddamar da ta shiga tsakanin gwamnatin jahar Kaduna da kuma kungiyar kwadago ta kasa ta NLC akan koran wasu ma’aikata.

Ministan kwadago Dr. Chris Ngige ya ce kawo yanzu dukkanin bangarorin biyu sun amince da kafa kwamiti mai mutane 10 inda bangaren gwamnatin jahar Kaduna ke da wakilai 6 ita kuma kungiyar kwadago nada wakilai 3 don samar da mafita game da ma’aikatan da aka sallama, wanda kwamitin zai gabatar da rahoton sa a ranar Talata mai zuwa.

Haka nan kuma an cimma matsayar cewar babu wani ma’aikaci da shiga yajin aikin da yayi zai shafi aikin sa.

Daga karshe an cimma matsayar cewar babu batun komawa ko kuma cigaba da wannan yajin aikin da kungiyar kwadago ta yi

Leave a comment