Kamfanin Taki Na Guarantee Ya Kudiri Aniyar Samar Da  Wadataccen Taki Ga Manoma


Daga Shehu Yahaya


A yayin da daminar bana ta fara kankama, kamfanin samar da taki na Guarantee ya bayyana aniyarsa na samar da wadataccen taki ga manoma wanda zai taimaka musu domin samun amfanin gona mai yawa.


Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin Alhaji Adamu Umar Yaro, a zantawarsa da manema a labarai inda yace kamfanin su  ya shirya tsaf wajen ganin ya samar da wadataccen taki ga manoma a fadin Arewacin kasar nan inda yace  suna samar da taki sama da buhu dubu 35 a duk mako wanda ake rabawa manoma a jihohin Arewa.


Alhaji Adamu Umar, yace kamfanin Taki na Guarantee ya himmatu wajen tabbatar da cewa sun kara inganta takin da suke samarwa, a cewarsa, sun tanadi injina na zamani wadanda zasu taimaka domin samar da taki mai inganci ga manoma.
Shugaban ya bayar da tabbacin cewa takin Guarantee shine zabin manoma a Arewacin kasar nan duba da yadda suke ingantashi.


Ya kara da cewa takin Guarantee ba  manoman Nijeriya  kadai suke amfani dashi ba harda na kasashen ketare irinsu Kasar Nijar da  sauransu yana mai cewa, suna samar da taki samfarin NPK 20-10-10 da 27-13-13 duk  domin amfanar manoma baki daya.
Da yake bayani akan masu gurbata takinsu suna sayarwa manoma, Alhaji Adamu Yaro, yace suna daukar matakan da suka kamata domin magance matsalar inda yace suna bukatar san hannun gwamnati a cikin lamarin.
Hakazalika, yace akokarinsu na kawar da zaman kashe wando ga matasa, kamfaninsu ya samar da guraban ayyukanyi ga matasa sama da guda dari wadansa wasunsu suna aiki kai tsaye da kamfanin wasun su kuma na wucin gadi ne.
Sai dai a bangare guda kuma kananan kamfanonin samar da taki a Arewacin kasar nan suna kokawa akan yadda jami’an tsaro suke matsa musu wajen karbar na goro musamman masu aiki a shiyyar Arewa maso gabas yayin da suke kai taki ga manoman shiyyar.

Leave a comment