Kungiyar Kananan Kamfanonin Samar Da Taki Na Bukatar Tallafin Gwamnati

Daga SHEHU yahaya

Kungiyar masu Kananan kamfanonin Samar da takin Zamani ( Small Scale Fertilizer Producers Association) ta bukaci gwamnatin tarayya data kawo musu dauki wajen ganin sun tsaya da kafarsu wajen ci gaba da samar da taki domin amfanar daukacin manoman kasar nan baki daya.

A wata sanarwa mai xauke da sanya hannun shugaban kungiyar Alhaji Umaru Alhassan, Wanda aka rabawa manema labarai a kaduna, sun bayyana cewa kungiyar  tana taka rawar gani wajen samar da taki musamman ga qananan manoma wadanda  suke Kwashe kaso mai yawa ga manoman kasar nan.

Alhaji Umaru Wanda kuma shine shugaban kamfanin Samar da taki Na Amfani, yace kananan kamfanonin Samar da Taki suke fitar da gwamnati Kunya wajen wadata manoma da Taki duba da yadda takin zamani Yayi tsada kuma kuma wani lokacin yanayin Karanci.

 Kungiyar tace baya ga wadata manoma da wadataccen Taki; tana samawa Matasa guraben aiki daga sassa daban- daban a fadin  kasar nan baki daya  Wanda hakan ya sanya suke kira ga gwamnatin tarayya data waiwayo su kamar yadda take bawa sauran bangarori tallafi domin suma su tsayu da kafarsu.

Shugaban yace a dai dai lokacin da damunar bana Ta fara kankama, manoma Taki mai saukin kudi da nagarta suke bukata  Wanda kuma babu inda zasu samu haka face daga qananan kamfanonin Samar da Taki domin sune suke sharewa qaramin manomi hawaye, hasalima, sune gatan qananan manoma a fadin kasar nan.

Sanarwa taci gaba da cewa “Ganin yadda gwamnatin Buhari Ta himmatu wajen bunkasa harkar gona hakan ya sanya mu masu kananan masana’antun samar  Taki muke Kira ga gwamnatin data sanya mu ciki jerin mutanan da take talkafawa domin ci gaban aikin gona”

“Kayan da muke sarrafa takin dashi Yayi tsada kuma takin mu a cikin farashi mai rangwami muke sayar dashi ga manoma, saboda haka muna bukatar tallafin gwamnatin Ta kowacce domin rage mana zafi duba da yadda muke Biyan kuxaxen haraji da kuma samawa matasa aikin yi. Muna ganin muma mun cancanci agajin gwamnatin tarayya” inji kungiyar.

Akan hakan mu ngiyar Ta bayyana gamsuwarta da yadda gwamnatin tarayya ta dukufa  wajen bunkasa aikin gona inda tace ya zama wajibi a jinjinawa shugaban  kasa Muhammadu Buhari bisa matakan da ya dauka Na Kawo ci gaban vangaren aikin gona a fadin kasar nan.

Kungiyar ta Sha alwashin wadata manoma da taki a wannan daminar a sassa daban-daban na kasar  nan domin koyi da matakan shugaban kasa  Muhammadu Buhari Na bunkasa  aikin gona musamman ga qananan manoma waxanda suke da kashi 70 cikin 100 Na  manoman dake kasar nan.

Alhaji Umaru Alhassan, Ya nuna damuwarsu dangane da masu gurvata Taki wadanda suke Amfani da buhun kamfanonin wasu suna zuba gurbataccen suna sayarwa manoma, lamarin da yace yana daga cikin matsalolin da suke ciwa kamfanonin Samar da taki Tuwo a Kwara.

Leave a comment