KADUNA 2023: Muna Son Dan Takarar Gwamna  Ya Fito Daga Shiyya Ta Daya- ‘Yan APC

Daga Shehu Yahaya

WASU masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da suka fito daga shiyyar ta daya a Jihar Kaduna sun roki Gwamna Nasir El-Rufa’i da ya ba shiyyar damar fitar da dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa domin yin gaskiya da adalci.

A cewarsu, an mayar da yankin saniyar ware idan ana maganar nade-nade duk da irin gudunmawar da suke baiwa Jam’iyyar da Jihar.

A wani taron manema labarai da suka gudanar a sakatariyar kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kaduna a ranar Litinin da ta gabata, wanda Ahmed Yahaya Lere da Usman Ahmed Danbaba suka yi jawabi a madadin masu ruwa da tsaki na shiyyar, sun bayyana cewa shiyyar su ce kashin bayan Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.

Sun ce “Hakika muna godiya bisa irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke yin ayyuka a ko’ina a duk fadin Jihar Kaduna da nufin kara inganta rayuwar al’umma baki daya, kuma hakan duk ya samu ne sakamakon irin cikakken hadin kai da goyon bayan da mutanen yankin shiyya ta daya suka dade su na bayarwa ga tafiyar wannan Gwamnatin APC”.

“Kowa ya sani cewa shiyyar mu ce ta fi karfi a Jihar, hakan ya faru ne saboda babu shakka ayyukanmu na ci gaba da yin fice a duk zabukan da suka gabata na 2015 da 2019 da kuma zabukan kananan hukumomi da aka yi kwanan nan.

“Wasu daga cikinmu a nan mun kasance shugabannin Jam’iyyar na Jiha da na shiyya, wakilan Jam’iyyar da suka dawo gida, tsofaffin Jami’an Gwamnati da ’yan takara, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, mun damu matuka da makomar Jam’iyyar tare da karfafa nasarorin da Gwamnatin Mallam Nasir Ahmad El-Rufa’i ta samu.

“Bayan doguwar tattaunawa da tuntubar juna a madadin jama’armu, mun bayar da kwarin gwiwa wajen neman wadannan abubuwa kan zaben wanda zai gaji shugabanmu, Malam Nasir El-Rufai.

Acewarsu, sun yi iƙirarin cewa suna da bukatar gwamna mai zuwa ya fito daga shiyyar saboda dalilai kamar haka.

Misali shiyya ta daya tana da Sanata, ‘yan majalisar wakilai shida, ‘yan majalisar dokokin waje goma sha daya, shugabannin kansiloli bakwai duk daga shiyyar ne.

Sai dai sun koka da cewa babu wani daya daga cikinsu a matsayin Gwamna, Mataimakin Gwamna, Ministoci biyu, Shugaban Jam’iyya, Sakataren Jam’iyya, Shugaban Mata, Shugaban Matasa ko kuma Wakilin Jiha a Jam’iyyar APC ta kasa daga shiyyar.

Sun kara da fayyace cewa su na sa ne fa yawan kuri’un da ake samu daga wasu yankuna a jam’iyyar APC raguwa kawai yake yi a koda yaushe, ” Amma yawan kuri’un da APC ke samu a yankin shiyya ta daya karuwa kawai abin yake kuma hakan a bayya ne yake, har ma karamar hukumar Zariya ita ta fi kowace karamar hukuma a Najeriya ba shugaba Bubari kuri’a a zaben da ya gabata ga dai misalai nan da yawa na cancantar kujerar Gwamna a APC sai shiyya ta daya.

Domin karfafawa da ci gaba da ayyukan yaba wa Gwamna a ‘yan kwanakin nan, ana bukatar dan takara wanda ya kware, mai taka rawar gani da kuma sanin tsare-tsare na gwamnatin Mal. Nasiru El-Rufai

Leave a comment