Kwastam Shiyyar Kano Da Jigawa Ta Kama Fatun Jaki Na Sama  Da  Miliyan  416, Ta Tara Haraji Na Biliyan 10.1

Kwantirola MA Umar

Daga Shehu Yahaya

Hukamar Hana Fasa-kwauri  ta Kasa shiyyar Kano da Jigawa   ta bayyana cewa  ta samu nasarar kama  fatun jaki guda 3,712 wanda kudinsu ya kai  sama da miliyan 416 da wasu haramtattun kaya.

Shugaban hukumar Kwantirola Mohammed Abubakar Umar, shine ya sanar da hakan lokacin da yake baje kolin kayan ga manema labarai a hedkwatar hukumar dake Kano. 

Hakazalika, yace hukumar ta Tara kudin haraji  sama da Naira biliyan 10.1 a cikin watanni uku da yayi da fara aiki a matsayinsa na Shugaban hukumar a shiyyar Kano da Jigawa.

 
Kwantirola MA Umar,  ya kara da cewa daga cikin kayayyakin da Hukumar Hana Fasa-kwauri ta  shiyar Jihar Kano da Jigawa ta kaman, har da Fatun Jakunkuna da suka kai kimanin guda 3,712  wanda adadin kudinsu ya kai Naira  416,382,278   wanda aka yi kokarinn fita da su zuwa Kasar waje, sai kuma shinkafar waje mai nauyin kilo 50 guda 1,031 da fakitin Taliyar waje guda 151 sai fakitin Macaroni guda 91.

Daga Hagu; Kwantirola MA Umar tare Da Mataimakin Kwantirola Sa’idu Alkali

Sauran kayan sum hada da; dilar gwanjo guda 131 da kuma shinkafar waje mai kilo 25 guda 3 da kuma sabulun wanki na waje guda fakiti 6.

Kwantirola MA Umar, yace daga kama aikinsa zuwa yanzu hukumar ta samu nasarar kara tara kudin harajin da take samu inda yace a shekarar data gabata hukumar ta tara biliyan 7 amma daga zuwansa cikin watanni uku sun tara Naira biliyan 10 da doriya.

MA Umar, yace zasu ci gaba da lalubo hanyar da zasu kara inganta samun kudadan haraji ta hanyar yin aiki kafada da kafada da sauran bangarorin hukumar dake aiki a shiyyar. 

Mota shake da Fatun Jaki

Yace hakan ya samu ne bisa irin kwarin gwiwar da shugaban hukumar kwastan ta kasa Hameed Ali yake basu ne, yana mai cewa zasu ci gaba da yin bakin kokarin su wajen tabbatar da cewa an hana fasa kwauri domin bunkasa ci gaba tattalin arzikin Nijeriya baki daya.

Ya kara da cewa hukumar kwastan shiyyar Kano da Jigawa, ta himmatu wajen ganin ta dakile ayyukan masu fasa akwauri inda yace jami’ansu suna aiki babu dare babu rana domin tabbatar da hakan.

Wani bangare na shinkafar waje da aka kama

Umar, yace zasuyi bakin kokarin su wajen ganin sunyi aiki da masu da tsaki a shiyyar wajen ganin hakarsu ta cimma ruwa akan samar da hanyoyin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasa baki daya.

Haka zalika, Kwantirolan ya yi kira ga ‘yan Nijiriya da su rika kiyaye doka, domin ko kadan bai kamata a ci gaba da shigo da ire-iren wadannan kayayyaki da aka san gwamnati ta haramta shigowa da su ba.

Leave a comment