Liman Ya Ajiye Limanci Saboda Shiga Takara A Katsina

Gwamna masari na jihar Katsina

Daga Mustapha Usman

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA Katsina ya ajiye muƙamin limancin saboda zai tsaya takara.

A lcewar Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA Katsina ya ajiye muƙamin limancin saboda zai tsaya takara.

A wasiƙar ajiye limancin da ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.

Wani ɓangare na wasiƙar, na cewa: Ni Muhammad Hashim (Liman) na aje muƙamina na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA saboda tsaya wa takara da zan yi.

“Ina fatan Allah SWT ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, ya yafe mana kura-kuren mu Amin.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ‘ƴan kwamitin masallacin da ma al’umma baki ɗaya.

Leave a comment