An Tsinci Jaririn Da Aka Jefar Da Shi A Bola A Abuja

An tsinci jariri a wani wurin zubar da shara a Kubwa, satellite area a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin yankin, Mustapha Ibrahim, wanda ya gano jaririn a safiyar ranar Talata, ya shaidawa City & Crime cewa ya je bahaya ne lokacin da ya ga jaririn.

Ibrahim ya ce, “Bayan na ga jaririn, sai na sanar wa jama’a. An ajiye wata leda cike da tufafin jarirai kusa da jaririn.

Amma mazauna yankin sun kai jaririn gidan marayu da ke Kubwa.

Wani mazaunin yankin mai suna Kehinde Ogundipe ya shaida wa manema labarai cewa irin wannan lamari ya faru watanni uku da suka gabata a yankin.

Leave a comment