Matawalle Ya Gwangwaje Sarakunan Zamfara Da Motoci Kirar Cadillac 2019

Sarkin musulmi Abubakar Sa’ad

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnan Jihar Zamfaran Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya raba motoci 260 ga daukacin sarakuna da iyayen kasa dake fadin jihar.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar shi ya kaddamar da rabon motocin a gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar a Jihar.

Sarkin ya bayyana jin dadinsa da jinjina ga Gwamna Bello Matawalle bisa yadda ya damu da jin dadin sarakunan gargajiya.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su ci gaba da ba gwamnatin Gwamna Matawalle goyon baya ta hanyar yin iya bakin kokarinsu wajen kawo karshen kalubalen da jama’a ke fuskanta Kan matsalar tsaro sake addabar al’umma.

A jawabinsa a wajen bikin, Gwamna Matawalle ya ce an yi hakan ne domin ganin irin matsayin da sarakunan gargajiya suke da shi a matsayin masu kula da addini da al’adu da kuma hanyar hada kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Matawalle ya ce, “A bisa la’akari da irin daukakar da gwamnatisa ke yi wa shugabanninmu da hukumominmu ne ya sa muka yanke shawarar sayo sabbin motoci kirar Cadillac 2019 Model ga sarakuna 17 da motocin Hyundai na manyan hakimai 13 da hakimai 230 a fadin kasar nan”.

Gwamna Matawalle ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da hada kai da shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Gwamnan ya Kara da cewa ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatina za ta ci gaba da yin aiki da daukaka martabar sarakuna gargajiya ta kowace hanya.”

Ya ce ” yanzu muna gyara tare da sake gina wasu daga cikin gidajen sarakunan mu a fadin jihar”. Yace “Wasu daga cikin wadannan ayyukan za a kammala su nan ba da jimawa ba”. Inji gwamna Matawalle .

Leave a comment