2023: Ban Son In Yi Gwamnan Katsina – Hadi Sirika 

Hadi Sirika

Ministan Sufurin jiragen sama kuma tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Katsina ta Arewa, Sanata Hadi Sirika ya ce shi yanzu baya son zama Gwamnan jihar Katsina. 

Majiyar mu ta samu cewa Ministan yayi wannan furucin ne a cikin wani faifan bidiyo da ya rika yawo a kafafen sadarwar zamani da ke dauke da Ministan a cikin shiga irin ta larabawa tare da wani mutum a wani wuri da muka kyautata zaton kasar Saudi Arabia ne. 

A cikin bidiyon, an ga mutumin da ke tare da Ministan ya na yi masaaddu’o’i ciki hadda ta zama Gwamnan jihar Katsina amma sai shi Ministan ya ce shi ba ya son zama Gwamna. 

“Ban Son Zama Gwamnan Jihar Katsina, Ina Addu’ar Allah Ya Biya Mani Bukatuna Na Alheri Ya Kuma Sanya Ni Aljannar Firdausi,” Inji shi a cikin bidiyon. 

Wannan dai a iya cewa ya kawo karshen rade-raden da ake yi tare da tunanin ko Sanata Hadi Sirika zai nemi kujerar Gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 dake tafe.

Sanata Sirika dai na daya daga cikin makusantan Shugaba Buhari kuma ya taka muhimmiyar rawa a mukamin sa na Ministan Najeriya. 

Leave a comment