Azumi 30 Za A Yi A Nijeriya Da Saudiyya

Wani shahararren masanin ilimin Sararin samaniya, ya yi karin haske kan yadda za a yi azumin bana 30 a Nijeriya da kasar Saudiyya.

Shahararren masanin, Adamu Dan Amurka ya bayyana hakan sannan kuma shafin sada zumunta na kwamitin ganin wata dake karkashin fadar Mai alfarma sarkin musulmi ya buga a shafinsa na Facebook.

Ya sake ikirarin cewa, za a samu kisfewar wata acikin watan Shawwal cikin ikon Allah.

“Idan baku manta ba tun shekaran da ta wuce lokacin da muka kammala Azumi 30 na sanar da ku cewa idan Allah ya kawo mu Wannan shekara, shi ma akwai wani Dama na sake samun Azumi 30 idan har an dauki Azumi a ranar Asabar (02/04/2022).

“Dukkan mu Nigeria da Saudiyya idan Allah ya kaimu ranar 29 ga Watan Ramadan, Wata zai riga Rana Faduwa.” Wani bangare na bayanan Dan America

Leave a comment