Hukumar Kwastam Shiyyar Arewa Ta Kama Buhunan Shinkafa 1,314  ‘Yar Waje A  Watan Afrilu 

Kwantirola Hamisu

Daga Shehu Yahaya 

Hukumar Yaki da fasa kwauri ta kasa Shiyyar Arewa mai hedikwata a Jihar Kaduna ( FOU ZONE B) ta kama Haramtattun kaya nau’uka 96 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 232 daga watan Maris zuwa Afrilun 2023.

Da yake baje kolin  kayan ga manema labarai a Kaduna, Kwantirolan hukumar mai kula da Shiyyar  Arewa wato ( FOU B) Albashir Hamisu, yace sun kama buhunan shinkafa ‘yar kasar waje guda 1,314 da Magungunar asibiti marasa rijista guda 219,000 sai katan na  Taliyar kasar waje guda 642 da jarkoki na man fetur mai nauyin lita 25  wanda  ajimlace kudinsu ya kai Naira 232, 530,050.42.

Shinkafa ‘yar waje da aka kama

Albashir Hamisu, ya kara da cewa manya daga cikin kayan da suka kama sun hada da buhuna 15 mai nauyin kilo 100 na Haramtattun wake da shinkafa ‘yar kasar waje sai kuma dilar gwanjo guda 94 da kuma tayar mota guda 49  da dai sauransu.

Kwantirola Hamisu,  ya godewa Al’ummar bisa irin goyon bayan da suke bawa Hukumar Kwastam na sanar da su muhimman bayanai dangane da yadda za’a magance matsalar fasa akwauri .

Taliya ‘yar waje

Hakazalika, ya godewa shugaban hukumar kwastan ta kasa Hameed Ibrahim Ali, bisa karin girma da yayiwa wasu jami’an hukumar wanda hakan zai kara musu kwarin gwiwar yaki da masu fasa kwauri a fadin kasar nan baki daya.

Leave a comment