Shugaban Karamar Hukuma Ya Rushe Gidan Liman Saboda Ya Soki Gwamnati A Gombe

Shugaban karamar hukumar Funakaye

A jiya ne shugaban karamar hukumar funakaye dake jahar gombe ya kaddamar da rushe gidan wani limami sakamakon waazi da yayi akan shugabanni.

Lamarin ya faru ne sakamakon zargin kwatanta da shugaban nin da azzalumai da limamin yayi Wanda hakan beyiwa shugaban karamar hukumar dadi ba.

Washe garin ranar asabar ne kuwa akaga katafila hade da jami’an tsaro sun dirarwa gidan liman inda suka ruguza gidan har kasa.

Munyi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar din amma abin yaci tura.

Amma da muka tuntubi limamin ta wayar tarho ya shaidawa wakilin mu tajuddeen koki cewa yana gida aka kawo masa takardar gayyata daga police station inda daga zuwansa aka dauki bayanansa aka kai shi kotu da laifin gini ba bisa ka’ida ba.

Limamin yakara da cewa alkali ya karanta min tuhuma ta inda nikuma na musanta amma duk da haka se aka hadani da ‘yan sanda tareda hukumar kula da gine-gine ta jahar gombe inda bamu tsaya ko ina ba se gidana Wanda a take aka rushe shi.

Leave a comment