Bikin Sallah:  El-Zakzaky Ya Rabawa  ‘Yan Jaridu Tallafi

Daga Shehu Yahaya

A ci gaba da shirye-shiryen bikin sallah da aka fara, Shugaban Majalisar ‘yan uwa Musulmi ta kasa (IMN)  Sheikh Ibraheem Yakubu El-Zazzaky , ya rabawa ‘yan jarida kayan abinci da kudin cefane domin gudanar da bakin sallah a Kaduna.

Sheikh El-Zazzaky, yace yayi hakan ne domin kara tallafawa ‘yan jaridu da abincin da zasu gudanar da bukukuwan inda yace suna taimakawa wajen bayar tasu  gudunmawar wajen fadakar da daukacin al’ummar kasa baki daya akan a Lamurran yau da kullum. 

Taron Rabon Abinci wanda ya gudana a harabar gidan Talabijin na AIT dake Kaduna a yau Alhamis,  wanda ya samu halarcin ‘yan jaridu sama da guda ashirin.

Abincin da aka rabawa ‘yan jaridar sun hada da shinkafa da madara da taliya da kuma kudin cefane.

Da yake jawabi Jim kadan bayan raba abincin,  Sheikh El- Zakzaky,  wanda Shugaban Cocin  Christ Evangelical and Life Church, Pastor Yohanna Buru, ya wakilta yace rabon kayan abincin sallah ba wai musulmai kadai aka bawa ba harda mabiya addinin Kirista dake fadin kasar nan  da ma kasar waje baki daya  domin murnar zagayowar bikin sallah karama.

Pastor Buru, yace  dalilin  da sanya El-Zakzaky  rabon abincin shine domin kara karfafa zamantakewa tsakanin mabiya addini musulunci da na kirista  wajen fahimtar juna a fadin kasar nan baki daya.

Buru, ya kara da cewa wannan rabon abincin ba shi bane na farko da Malamin yake ba, tsawon shekaru yana gudanqar da shi musamman lokutan watan azumin Ramadan da bikin sallah wanda miliyoyin ‘yan Nijeriya suke amfana dashi ko lokacin da yake tsare a gidan gyaran halin  kaduna har zuwa yanzu.

Sai dai Pastor Buru,  yace bisa tsadar kayan masarufi da matsalar corona ya kawo dan cikas a shirye-shiryen bikin sallah bana.

Ya kuma taya daukacin al’ummar musulmai murnar zagayowar wannan sallar inda ya bukaci su da suyi koyi da darussan da suka koya a cikin azumin watan Ramadana, musamman wajen kara tsoron Allah da kyautata dangantaka a tsakanin mabiya addinai daban-daban a fadin Nijeriya. 

Akan ya bayyana takaicinsa dangane da yadda lamurran tsaron kasar suke kara lalecewa inda akwai bukatar Gwamnati ta kara samar da matakan gyara domin ceto rayuwar al’umma baki daya daga cikin wannan matsalar. 

Leave a comment