Gwamnatin Kaduna Ta Haramta  Zanga-zangar Addini  a jihar 

Daga shehu Yahaya 

Biyo bayan zanga-zangar data varke a jihar Sakkwato bisa kisar wata baliba da ta aibanta Manzo, Gwamnatin jihar ta haramta duk zanga-zangar addini a faxin jihar.

A wata Sanarwar da kwamishinan harkokin tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya rabawa manema labarai a yammacin yau asabar yace duk wanda aka kama da karya doka zai fuskanci fushin hukuma.

Aruwan yace bayan zaman tuntuva da vangaren jami’an tsaron jihar sun yanke shawarar xaukar matakin hana duk wata zanga-zangar addini nan taki.

Yace xaukar matakin ya zama dole bisa la’akari da abubuwan da suke faruwa a Arewacin qasar na rashin zaman lafiya.

A cewarsa, gwamna Nasiru El-Rufai ya biqaci duk bangarorin tsaro da su zauna da shirin ko ta kwana wajen dakile duk wata kungiyar da zata fito domin gudanar da zanga-zanga a jihar.

Yace gwamnatin jihar Kaduna tana Jan hankalin.malaman addini musulunci nada Kirksta da su ci gaba da fadakar da mabiyansu akan illar fitowa domin gudanar da zanga-zanga wanda ka iya jefa jihar wani mawuyacin hali.

Gwamnatin  ta buqaci xaukacin al’ummar jihar da su ci gaba da samar da abubuwan da zasu kawo zaman lafiya a jihar, kuma su sanar da jami’an tsaro rahoto akan duk wani ko wata kungiya da ke nufin kawo  rashin zaman lafiya a jihar.

.

Leave a comment