Kungiyar NUJ Ta Karrama Farmtrac Bisa Ciyar Da Jihar Kaduna Gaba

Daga Shehu Yahaya 

Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Kaduna,  Ta bayyana gamsuwarta dangane da irin gudunmawar da kamfanin Farmtrac yake bayarwa wajen ciyar da jihar Kaduna gaba .

Shugabar kungiyar ta (NUJ )Hajiya Asma’u Halilu,  itace ta bayyana hakan Jim kadan bayan  kungiyar ta karrama shugaban kamfanin Farmtrac Injiniya Sadiq Abubakar da lambar yabo a wani taron lacca da kungiyar ta shirya  a sakatariyar kungiyar dake Kaduna.

Hajiya Asma’u Halilu, tace Kamfanin na Farmtrac ya jagoranci aiwatar da ayyuka masu inganci da Nagarta na raya jihar Kaduna da samawa matasa ayyukan yi daban-daban wanda hakan ya sanya kungiyar ta karrama shugaban kamfanin domin kara masa qwarin gwiwa wajen ganin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan masu inganci da Nagarta a fadin jihar baki daya.

Shugabar tace kungiyar NUJ tana zaqulo mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen ciyar da jihar Kaduna da al’ummar gaba domin basu lambar yabo wanda hakan zai kara musu kwarin gwiwar ci gaba da abubuwa masu kyau da sukeyi.

Da take bayani dangane da zaben 2023 mai zuwa, tace ‘yan jarida suna da rawar takawa wajen samar da shugabanni na gare masu kishin son ci gaban kasar,  inda tace yada manufofin ‘yan siyasa. 

Akan hakan ta bukaci daukacin kafafen yada labarai da su Zuma masu taka tsan-tsan wajen yada manufofin ‘yan siyasa da zasu taimakawa al’umma ba da kuma kaucewa yada labarai masu tada hankali da labarai masa sahihanci.

Kamfanin FARMTRAC yana daga cikin kamfanin da gwamnatin jihar kaduna take bawa aikin hanyoyi wanda hatta gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufai ya bikaci sauran kamfanonin cikin  gida da suyi koyi da Farmtrac wajen gudanar da nagartattun ayyuka a fadin jihar.

Da yake jawabi Jim kadan bayan ya karbi lambar yabon, Injiniya Sadiq Abubakar,  ya godewa kungiyar ta NUJ bisa karramawar da suka yiwa kamfanin Farmtrac inda yayi alqawarin ci gaba da gudanar da ayyuka masu inganci kamar yadda suka saba.

Leave a comment