TALLAFAWA AL’UMMA: An Karrama Dan Bichi Da Lambar Yabo

 

Dan Bichi rike da lambar Yabon

Daga Shehu Yahaya

Kungiyar ‘yan jaridu na Arewacin Nijeriya (NTJ) ta karrama Dan kishin Kasa Alhaji Salisu Abubakar, da lambar yabo bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da dorewar shirin rabon abinci na daliban makarantun firamare na gwamnatin tarayya ya gudana cikin nasara a karamar hukumar Dala dama jihar Kano baki daya.

Alhaji Salisu Abubakar wanda akafi sani ( Dan Bichi) wanda kuma shine mataimakin kwamitin kula da raba kayan abinci ga daliban makarantun firamare na karamar hukumar Dala, ya samu lambar yabon ne bisa irin rawar da ya taka wajen tabbatar da cewa shirin ya samu nasara da kuma kokarinsa na tallafawa marasa karfi a jihar Kano baki daya.

Da yake mika lambar yabon shugaban kungiyar Alhaji Mukhtar Maitama,  yace binciken da ‘yan jarida suka gudanar a kananan hukumomi 44 na jihar  Kano sun gano cewa babu wata karamar hukuma da ta kai ta Dala wajen kwatanta adalci domin tabbatar da samun nasarar shirin rabon abinci wanda kuma Alhaji Salisu Abubakar yana kan gaba wajen ganin shirin ya kai ga cin nasara.

Shugaban wanda Sani Haladu, ya wakilta yace a binciken da suka yi sun gano cewa Alhaji Salisu Abubakar yana daya daga cikin muhimman mutane a  jihar Kano da suka damu da ci gaban al’ummar wajen tallafawa marasa karfi da kuma taka-tsan-tsan da dukiyar gwamnati wanda hakan ya sanya suka karrama shi da lambar yabo ta girmamawa.

A nasa jawabin Sakataran Ilimi na karamar hukumar Dala Alhaji  Mohammed Abba Sanka,  ya jinjiwa kokarin kungiyar ‘yan jaridar wajen zakulo Salisu Abubakar domin bashi lambar yabo inda yace basuyi zaben tumun dare ba, hasalima, sunyi abin akan gaba kuma akan lokaci.

Alhaji Mohammed Abba Sanka,  wanda shine shugaban kwamitin rabon kayan abinci na karamar hukumar Dala, ya kara da cewa duk nasarar da kwamitin ya samu akwai gudunmuwar Salisu Abubakar wanda yake aiki babu dare babu rana domin tabbatar da shirin ya kai ga cin nasara.

Ya kuma godewa kungiyar da sukeyi tunanin karrama abokin aikinsa bisa jajircewarsar waje   bayar da tasa gudunmuwa domin ciyar da jihar Kano gaba wanda hakan abin alfaharine.

Yace al’ummar jihar musamman kwamitin kula da rabon kayan abinci tun daga matakin jiha har ga karamar hukuma ba zasu manta da gudumawar da Salisu Abubakar yake bayarwa

Leave a comment