Mabiya Darikar Shi’a a Nijeriya Sun Kafa Dandamalin Siyasa

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Daga Idris Umar,Zariya

A cikin satin daya gabata ne mabiya darikar Shi’a a Nigeriya karkashin jagorancin Sheik Ibrahim El-Zakzaky suka fitar da wani rahoto mai dauke da sa hannun Kwamret Shuibu Isa Ahmad kodineto na tafiyar a kasa baki daya.

Ga bayanin kai tsaye don masu karatunmu kamar haka.

Da sunan Allah mai Rahma mai jin ƙai.

Dandamalin Siyasar Harkar Musulunci dandamali ne wanda yake ƙarkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).

Maganganu na rashin fahimta sun dinga yawo dangane da sabon Dandamalin Siyasa na Harkar Musulunci a Najeriya da aka kaddamar kwanan nan. Wannan shi ne ya wajabta fitar da wannan maƙalar don yaye shubuha, don muna da tabbacin cewa mafi yawancin gunagunin sun faru ne saboda rashin fahimta.

Yan makonnin da suka gabata aka ƙaddamar da Dandamalin Siyasar, bayan doguwar tattaunawa da aka yi tare da Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H). Dandamalin ya kunshi wadannan manufofin:

√ Kiyaye haƙƙoƙin ‘yanuwa da kuma manufofin Harka din.

√ Samar da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa tsakanin mutanen da ke zaune a wannan kasa din Najeriya.

√ Tabbatar da daidaito wajen rabon arziƙin ƙasa.

√ Kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

√ Kiyaye alaƙa ta diflomasiyya da kuma yunƙurin samar da adalci a tsakanin al’umma.

√ Wayar da kan al’umma akan haƙƙoƙi da nauyikan da suka hau kansu, da sauransu.

Ƙari akan manufofin da aka ambata a sama, Dandamalin Siyasar zata taimaka wajen yin aiki don dakatar da ayyukan wasu mutane waɗanda suke yawo suna aikata wasu ayyukan da basu dace ba da sunan Harkar Musulunci.

Saboda haka, an samar da dandamalin ne don tattaro wasu sashe na mutane, mabiya Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) domin yin aiki dasu.

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya shahara a matsayin jigo wajen aikata ayyuka na alheri da ɗan-adamtaka, gami da goyon bayan adalci da daidaito. A wurare da dama, an sha ganinsa yana miƙa hannun taimako na kuɗi da kariya ga mabuƙata, musamman a lokutan faɗace-faɗacen ƙabilanci da ma rikicin bayan zaɓe. A soboda haka, bai kamata ya zamo abun mamaki ba don an ga ya amince da yunƙurin ƙaddamar da Dandamalin Siyasa na Harkar Musuluncin.

Tun daga ranar da aka kafa Dandamalin Siyasar, ta kasance tana gudanar da ayyukanta ne bisa sa idon Jagoran Harkar Musuluncin, kasancewar shi ne yayi ƙarin haske akan ƙa’idoji (principles) da hanyoyin cimma hadafi (policies) na Harkar Musuluncin, tare da bayani akan matsayin ayyukan siyasa a cikin harkar. A cewarsa, wasu ayyukan zasu iya zama Wajibi ko Mustahabbi , ko kuma ma Haramun, gwargwadon yanda yanayi da hali ya bayar. Sa’annan kuma ayyukan Dandamalin ba zai zamo ya saba da ɗaya daga ginshiƙan ƙa’idojin Harkar Musulunci ba.

Hasali ma, ya dace da mahangar Annabinmu mai daraja, na cewa bai kamata a dinga ma Musulunci kallon umurni da hani ko kuma wani irin tsari na falsafa kawai ba, kamata yayi a kalle shi a matsayin tsarin tattara komai-da-komai wanda ya ƙunshi ɓangarorin gudanarwa da zamantakewar al’umma mai ƙarfi.

Ayyukan Dandamalin Siyasar zai dinga zagayawa ne a al’amuran diflomasiyya, don samar da hanyar cimma zaman lafiya a zamantakewar al’ummar Najeriya, tare da kiyaye sheƙar da jinaine da zalunci na ba-gaira ba-dalili da hukumomin Najeriyar ke yi.

Ba abun mamaki bane ya zama mutane sunyi ma Dandamalin gurguwar fahimta a matakin farko. Don kiyaye hakan ne ma yasa muka gabatar da wasu ziyarce-ziyarce a wasu wurare don wayar da kan mutane akan ayyukan Dandamalin.

Tare da girmamawa duk wani wanda ya kasance cikin wannan tafiya ta Political Forum ya ya kaice ma principles da policies na Harka Islamiyya da kuma hadafofin forum din, to zamu barranta daga ayyukansa. Sakamakon hakan ne yasa muke roƙon cewa duk wanda yake da wasu tambayoyi akan Dandamalin Siyasar ya gabatar dasu zuwa ga masu gudanarwa na CWC da aka tanadar, waɗanda sunayensu da lambobin wayoyinsu ba ɓoyayyu bane.

A ƙasa akwai lamba da adireshi imel ɗin da za’a iya tuntuɓa kafin a saki cikakken jadawali (na tsare-tsare) a nan kusa.

08142144440 ko imel ta wannan adireshin; politicalforum14@gmail.com

Sa hannu:

Shuaibu Isa Ahmad
Mai gudanarwa na ƙasa (National Coordinator)

Wannan bayani ya ja hankalin mutanen kasar baki daya tare da yiwa mabiya darikar ta Shi’a tambayoyi kamar haka.

Shin yan Shi’a zasu shigo siyasar ne dumu-dumu kamar yadda ake gudanarwa a yanzu APC da PDP ?

Hakan ba zai canza mufar kiran Shaihin malamin nasu ba?

Hakan yasa wakilinmu yayiwa wani mabiyin darikar ta Shi’a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky mai suna Umar Idris.

Kwamret Umar yace, babu abin da zai canza manufar kiran jagoransu Sheik Ibrahim El-Zakzaky.

Domin yin mu’amula don kare mutunci da yiwa kasa hidima ba zai canza manufar tafiyarba sai daima manufar ta kara kyau da haske ga jama’a domin manufa daban mu’amula daban don munce zamu shiga siyasa ba yana nufin mun canza daga manufarmu da akasammu ada bane a a zamu kawata manufar tamune wato yin gogaiya da mutane da taimaka was nuna da bin masu hakkokinsu bazai hanamu bin ginshikin rayuwarmuba wato abin da Allah ya halicceka dominsa kokarin tabbatan addini

Dominma gogaiyar ce take kara maka kwarin guiwar cimma manufa wato abin da kasa a gaba.

Sai tambaya ta biyu da mafiya yawan mutanen kasan keyi akan wannan sabon al’amarin shine wace jambiya yan Shi’ar zasubi?

Tambayar da wakilinmu ya kara jefawa kwamret Umar kenan a matayinsa na mabiyin Sheik Ibrahim El-Zakzaky

Mu kamar abin da aka doramu akai wanda kuma shi muke ganin a matsayin siyasar mai tsafta da akeyi a sauran kasashe na duniya masu yiwa yan kasansu adalci mamar janhuriyar musulunci wato Iran.

Ya zamana mun shiga cikin al’umma muyi mu’amala mai kyau har in zabe yazo kuma dama ya bayar sai mu goyi bayan duk mutumin da mukaga zai yi adalci ga jama’a ba tare da mun kafa jambiyaba ai cikinmu akwai wandanta suka karanci siyasar da matsayinsu ya kai matsayi a jami’o’i

Haka zilika a cikin gudanar da siyasar tamu zamu ki marawa duk wani mai burin kwashe dukiyar kasa don biyan bukatar kansa.

Kuma zamu dukufa wajan zakulo hanyar sulhu a tsakanin al’umarmu na kasa baki daya tare da yin adalci a tsakakin al’umar kasa baki daya.

Kwamred Umar ya karkare da cewa su mabiya Sheik Ibrahim El- Zakzaky ba su bukatar kafa jambiya amma suna tare da duk wanda zai kare mutuncin al’umma kamar yadda doka ta shinfida.

Tuni dai bincike ya tabbatar da cewa mabiya darikar ta Shi’a a Nigeriya karkashi jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky sunyi nisa da gudanar da tsare tsare wanda zai basu damar gudanar da manufofinsu ingantattu da kowa zai amfana dashi a cikin al’umma tun daga mazabu har zuwa jiha har kasa baki daya.

Ya zuwa hada wannan labarin bincike ya nuna cewa tuni manya daga bangarorin siyasar kasanne ke zuwa ga shugaban na mabiya darikar ta Shi’a wato Sheik Ibrahim El-Zakzaky don tattauna muhiman muhimman abubuwa

Daga cikin manyan mutanen da ake da tabacin zuwansu wajan Shaihin malamin akwai manjo Hamza Almustafa dogarin marigayi tsohon shugaban kasarmu Nigeriya Janaral Sani Abacha da Halaji Buba Galadima na hannun daman shugaban kasa a lokutan baya wanda duk sun ziyarci shi jagoran yan’uwa musulmin mabiya darikar ta Shi’a a Nigeriya a gidansa dake Abuja kwanakin baya.

Ganin wannan cigaba da aka samu ne jama’a keta jiwa jagoran yan’uwa Musulmin fatan alheri a shafukan sada zumunta.

Leave a comment