Sarkin Kano Ado Bayero Ya Yaba Da Gudummawar Masu Yiwa Kasa Himida

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare masu yiwa Kasa hidima a fadarsa Dake Kano

Daga Shehu Yahaya

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace masu bautarwa kasa suna da matukar muhimmanci a kasar nan duba da yanda suke zuwa daga jihohi daban daban.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin tawagar kungiyar dalibai musulmi da suke hidumtawa kasa a jihar nan yayin da suka kai masa ziyara fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace tun a shekarar 1974 aka samar da hukumar dake kula da masu hiddumtawa kasa domin hada kan al’ummar kasar nan, inda ya yabawa gwamnatin da ta samar da shirin hidumtawa kasar.

A nasa jawabin shugaban kungiyar musulmi masu hidumtawa kasa Muhammad Sulaiman yace kungiyar na aikin shiga kauyuka domin ilimantar da al’umma tare da koyar da daliban makarantun primary da sakandire.

A wani cigaban kuma shugaban Hausawan kasar Ghana Muhammad Sa’id ya ziyarci fadar Sarkin Kano domin shaidamasa cewa sun samar da wani gari da za su sanya masa suna kanon dabo a can kasar ta Ghana.

Leave a comment