Da Ikon Allah PDP Zata Kawo Karamar Hukumar Giwa — Inji Kago

Honarabul Shehu Bello Kago

Daga Idris Umar,Zariya

Mataimakin shugaban kwamitin yakin zaben jambiyar PDP a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna Honarabul Shehu Bello Kago ya tabbatarwa manema labarai cewa, da ikon Allah jambiyar PDP ne zata yi nasara a kowani mataki na karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Honorabul Kago yayi wannan bayaninne jim kadan bayan karbar yayan jambiyar APC guda dari 200 zuwa PDP cikin harda honorabul Kabir Tsoho Yakawa da wasu jiga-jigai da suka biyoshi daga APC da dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jambiyar PDP Alhaji Isa Ashiru Kudan ya karbesu tare da yi masu wankar tsarki a karamar hukumar tasu ta giwa.

Honorabul Shehu Kago yace duk mai hankali ya kamata ya gane cewa zaben 2023 PDP ce zatayi nasara a dukkan kujerun da take nema bisa yadda alamu ke nunawa.

Mataimakin shugaban yace, bubban misali ga jama’a shine yadda mutane ke ficewa daga wata jambiyar suna komawa janbiyar tasu ta PDP mai albarka a halin yanzu.

Yace ba komi yasa jama’ar ke facewa daga wasu jambiyunba face irin riko da adalci da jambiyar tasu ta PDP ke yiwa jama’a a lokutan baya da kuma wannan lokacin.

Karshe Honorabul Kago ya nemi matasan karamar hukumar giwa dasu guji yin bangar siyasa, yace kada su yarda wasu yan’ siyasa suyi amfani dasu wajan cin zarafin jama’a a yayin da ake gudanar da yakin neman zaben a kowani mataki

Kuma yayi fatan Allah ya baiwa PDP nasara tare da fatan samun tabbatarccen zaman lafiya a karamar hukumar Giwa da kasa baki daya.

Honorabul Kago ya rike mukamai da dama a karamar hukumar tasu ta Giwa.

Honorabul kago shine Codineto na Atiku Mandate Group Giwa.

Kuma ya rike mukamin shugabanin PDP Stockholders na karamar hukumar Giwa

A yanzu haka ubane a PDP United Forum Giwa local government Kaduna state.

Leave a comment