PDP Ce zata sharewa matasa hawayensu Inji — Dakta Talba

Daga Idris Umar,Zariya

Darakta janar na Atiku project Dr Hamza Talba ya tabbatar da cewa kashi 60 cikin 100 a tafiyar dan takarar shugaban kasa a jambiyar PDP Alhaji Atiki Abubakar na matasane da mata in Allah yasa suka sami nasara.

Talba yayi wannan jawabin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tattauna hanyar magance matsalolin dake Addabar arewacin Nijeriya da ( Coletion of Arewa Student and Youth Initiative) wato hadakar kungiyar dalubai da matasan Arewa na kasa da ya gudana a dakin taro na Arewa House dake Kaduna a cikin wannan satin.

Dakta Hamza Talba masanine a harkar siyasa kuma kwarerre cikin masu marawa tafiyar Alhaji Atiku Abubakar a matsayin Dan takarar shugaban kasan Nijeriya a 2023.

Tuni Talba ya tabbatar da cewa da ikon Allah PDP zatayi nasara kuma itace zata kori yinwa da rashin tsaro dake addamar wannan kasar tamu Nijeriya.

Yayi fatan matasa zasu dunkule guri guda don fitar da murya kwara daya tak wanda hakan shi zai taimaka masu wajan samun nasara a fafutukar da sukeyi a kasa baki daya kuma ya tabbatar da cewa PDP zata share masu hawayensu kuma yayi kira dasu ba jambiyar PDPn goyon baya don kawo sauyi mai inganci a kasa baki daya.

Leave a comment