Ilimi Shine Ginshikin Rayuwa – Chidari

Daga Shehu Yahaya

An bayyana cewar samar da Jami’oi masu zaman kansu yana da matukar tasiri wajen cigaban ilimi tare da gina Al’umma.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Engineer Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana haka lokacin da ya ke karbar bakuncin Shugabannin gudanarwa na Jami’ar Baba-Ahmed da ke nan birnin Kano wadanda su ka kawo ziyara zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano

Engineer Hamisu Ibrahim Chidari ya ce bisa la’akari da dimbin yawan Al’ummar Jihar nan akwai bukatar samar da irin wadannan jami’oi domin bunkasar Jihar nan.

Haka kuma ya bayyana cewar bisa la’akari da mahimmancin ilimi wajen cigaban Al’umma ya sa gwamnatin Jihar Kano bisa jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta ke baiwa sashin ilimi fifiko na musamman wanda hakan ya sa ko a wannan kasafin kudi na bana na Jihar Kano,bangaren ilimi ya sami fifiko akan sauran sassan kasafin kudin.

Kazalika ya godewa jagororin wannan Jami’a bisa wannan ziyara tare da tabbatar musu da cewar Majalisar na tare da su a duk Al’amuran da su ka shafi cigaban Al’umma

A jawabinsa, Shugaban Jami’ar Farfesa A.I.Tanko ya ce makasudin zuwansu shi ne domin kara dankon Zumunci tsakanina Jami’ar ta BABA-AHMED da Kuma Majalisar Dokokin Jihar.

Haka kuma ya godewa Yan Majalisun bisa yadda su ke kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu musamman gudanar da doka da wakilci da kuma sanya idanu akan ayyukan gwamnati a kowane lokaci.

Leave a comment